Kamfanin Facebook ya kare kanshi dangane da zargin da ake mishi na cewar ya kan bar wasu abokan hurdar shi suna satar bayanan jama’a, ko bayanan abokansu batare da sannin suba.
A ranar Talata jaridar New York Times ta ruwaito cewar kimanin wasu kamfanoni 150, da suka hada da kamfanin Amazon, Netflix da Spotify- suna nadar bayanan jama’a a shafukansu harma da na abokansu.
jaridar ta kara da cewa, wani babbabn abun kunya shine yadda kamfanin ke satar bayanan jama’a, kana da yin amfani da data ta yanar gizon jama’a, kamar yadda su kayi a lokacin zaben Amurka na shekarar 2016.
Shugaban tsare-tsare na kamfanin Konstantinos Papamiltiadis, ya shaida cewar wannan ba wani abu bane, illa hanyar inganta danganta tsakanin mutane da kuma waddannan kamfanoni da suke mu’amala dasu, wajen saye da sayarwa.
Kamfanin kan bada irin wannan damar ne kawai ga wasu tsirarun kamfanoni, da mafi akasarin mutane suke da wata alaka, kodai na siyayya ta yanar gizo, ko danganta wajen kasuwanci.
Ya kuma kara jaddada cewar, babu wani wanda yake bada bayanan mutane batare da izinin suba, duk lokacin da suka bada bayanai, tabbas mutane ne ke amsa cewar a bada, don haka su kuma suke badawa.