Kamfanin Facebook ya kaddamar da wata sabuwar hanya da za ta rika taimakawa mutane samun muhimman abubuwa kamar abinci da ruwa da kuma mafaka a duk lokacin da wata annoba ta auku.
Wannan hanya da kamfanin ya samar wacce aka yiwa lakabi da “Community Help” wato taimakon al’uma, zai ta rika hada kan mutane dake kusa a yankin da annoba ta fadawa su nemi taimako, ko kuma a samu damar mika taimako ga masu bukata.
Duk masu shafin Facebook da ke yankin da annobar ta fadawa za su sami damar shiga wannan bangare da aka kaddamar, wanda zai hada su da wasu mutanen dake kusa da su wadanda za su taimaka musu da abubuwan da suke bukata kamar abin hawa da kayayyakin jin ‘kai.
Wannan bangare dai na na tallafawa al’uma zai zo ne karkashin maballin Safety Check, idan mutum ya sabunta manhajarsa wato ya sauke sabon update.
Yanzu haka dai an kaddamar da wannan fasaha ne a wasu kasashe shida, ciki har da Amurka da India da Saudi Arabia, ana kuma shirin fadada ta zuwa sauran kasashe bayan kwashe ‘yan makonni ana gwaji.
Your browser doesn’t support HTML5