Facebook Ya Fito Da Sabon Tsarin Yadda Labarai Zasu Dinga Bayyana

Kamfanin Facebook ya kammala shiri tsab, don jagorantar sabon tsarin tace labaran da zasu bayyana a shafin mutane, cikin tsarin kamfanin na bayyanar da komi batare da boye-boye ba.

Sabon tsari da aka kira “Me yasa nake ganin wannan?” jiya Litinin tsarin ya fara aiki, wanda zai bayyanar da yadda labarai ke tafiya da suka hada da bidiyo, hotuna duk da zasu dinga bayyana a gefen labarai a shafin mutun.

Babban dalilin shine mutane zasu dinga ganin dalilan da suka sa labarai na musamman ke bayyana a shafukan su. Kuma zai basu damar canza yadda bayanan ke fitowa a shafukan nasu, ta yadda zasu sauya wani nau’in labari ya dinga fitowa madadin wanda ke fitowan.

Mutun na da hurumin zabar nau'in labarin da zai bayyana a shafin sa a duk lokaci zuwa lokaci.

Shugaban sashen labarai na kamfanin Facebook John Hegeman, ya bayyana haka jiya Litinin. Ya kara da cewar biyo bayan rikice-rikice da kamfanin ya fuskanta cikin ‘yan watannin baya, shi yasa suka fito da sabon tsarin don maido da martabar kamfanin a idon duniya.