SAN FRANCISCO – Nan ba da daɗewa ba, za ku lura cewa tallace tallacen da kuka saba gani suna bin ku a yanar gizo ko a facebook, za su ragu.
Dandalin Facebook zai ƙaddamar da wasu hanyoyin cika alkawarin da ya yi alkawarinsu tun da dadewa na ba da damar hana kansa iya tattara bayanai game da ku akan shafinku na yanar gizo daga manhajoji waje.
Kamfanin ya fada a jiya Talata cewa yana kara wani sabon fanni inda za ku iya ganin duk abin da Facebook ta ke bibiye da shi na masu binku a duk lokacinda kuka danna alamar "like" da sauransu. Amma za ku iya zaɓar kashe manhajar toshewar in ba ku so, in ba haka ba, masu bibiyar za su ci gaba da yi, kamar yadda suka saba.
Wannan abin da aka fi sani da lakabin "clear history," wato goge tarihin na wasu shafuka da ka ziyarta, yanzu zai koma amfani da wani sabon sunna wai shi “off-facebook activity.” Tun daga ranar Talatar nan za’a soma ganin wannan sabuwar manhajar a kasashen Koriya ta Kudu, Ireland da Spain ranar Talata. Kamfanin bai ba da lokacin da zai soma aiwatarda wadanan chanje-chanjen a Amurka da sauran kasashe ba, kawai cewa yayi za’a ga abin a cikin "watanni masu zuwa."