Facebook Ya Fitar Da Manhaja Dake Bankado Hoton Tsiraicin Kananan Yara

Tambarin Facebook

Jiya Laraba kamfanin Facebook ya bayyana cewa wata sabuwar manhaja dake bankado hotan tsaraicin kananan yara, ta taimakawa kamfanin wajen cire hotunan yara har miliyan 8 da dubu 700 a cikin watanni uku da suka gabata.

Wannan manhaja da Facebook ya ce ya samar tun shekarar da ta gabata, tana taimakawa matuka wajen gano wasu abubuwan da basu kamata ba, ta hanyar tantance dimbin hotunan dake shafin Facebook.

Kamfanin ya ce ya kara matakan lura da duk abubuwan dake shafin, a kokari da yake na tabbatar da ganin babu sauran hotunan tsaraicin yara a shafin, haka kuma shirin zai taimakawa Facebook wajen horar da ma’aikatansa dake aikin zakulo ire-iren hotunan cikin gaggawa kan biliyoyin hotunan da masu amfani da shafin ke kafewa a kullum.

Facebook yace zai yi amfani da fasahar da kafar Instagram.