Kamfanin Facebook yayi alkawarin chanza tsarin kare bayanan shafin san a dandalin sada zumunta, domin samar wa mutane hanyar goge bayanan su cikin sauki a yayin da ake ci gaba da cece kuce akan sirrin masu anfani da shafin da ake da dandalin ke dauka.
Kamfanin yace zai fito da sababbin kayan aki da zasu baiwa masu amfani da shafin damar ganin kowanne bayani dake kunshe a dandalin, har ma su iya daukan shi su kuma lalata shi. Zai kuma bawa masu amfani damar maida bayanan zuwa wani shafin sada zumunta idan suna da bukatar barin facebook.
An tsara Chanje chanjen yadda zasu bi sabon tsarin kare bayanai na turai ba wai saboda sukar da sukai ta sha ba, biyo bayan bayanan da aka ce kamfnin sarrafa bayanai na Cambrige Analytica ya sata, a cewar kanfanin na facebook.
Your browser doesn’t support HTML5