WASHINGTON, D.C. —
Kamfanonin Facebook, YouTube, Twitter da na biyan kudi Venmo na neman kamfanin tattara fasahar fuska da ya dakatar da girke manhaja mai gano mutanen da ke cikin hotuna, wanda yanzu haka suke aiki hannu da hannu da jami’an ‘yan sanda.
Facebook ya bukaci kamfanin “Clearview AI” na birnin New York da ya daina zuwa ko kuma amfani da bayanai daga shafin sa da kuma shafin Instagram.
Kakakin kamfanin ya ce "daukar bayanan mutane ya sabawa manufofinmu."
Kamfanin Clearview ya fuskanci binciken kwakwaf tun bayan fitowar wani rahoto da kamfanin dillancin labarai na New York Times da Buzzfeed suka fitar, da yake bayyana yadda yake hada kai da jami’an tsaro, da kuma aikata wasu ayyuka na lalata kafofin watsa labaru da sauran hanyoyin yanar gizo.