Kamfanin Facebook ya sake yunkura wajen yaki da labaran boge da ake kira Fake News a turance, ta hanyar aika wasu labaran Facebook zuwa kamfanin dake tantance sahihancin labarai, a kuma saka sakamakon da kamfanin ya samo a ‘kasan kowanne labari.
A wata sanarwa da kamfanin ya fitar ta shafin yanar gizo, Facebook zai fara amfani da manhajar da zata rika bankado labaran da suka yi kamar na boge, a kuma aika shi ga kamfanonin da su rika tantance labaran.
An dade ana sukar Facebook da cewa ta kafar ne ake yada labaran boge a duniya, wanda kuma ake tunanin shine ya sauya akalar zaben shugaban kasar Amurka da aka gudanar a shekarar 2016.
Batun labaran bogi ya zamanto babban batu a fagen siyasar Turai, inda Faransawa suka rika samun labaran karya ana dab da zaben shugaban kasar Faransa a watan Mayu. Haka kuma kasar Jamus ta goyi bayan cin tarar duk kafar sada zumuntar da aka samu da laifin kin daukar matakin goge duk wani abu da aka kafe bai dace ba.
Yanzu haka dai Facebook ya ce zai ci gaba da gwajin duk wasu hanyoyi da zasu taimaka wajen rage yawan labaran karya da ake kafewa a kafar.
Your browser doesn’t support HTML5