Yawan masu amfani da shafin Facebook na dab da kaiwa Biliyan biyu, wanda hakan ke zamantowa wani abin tarihi da zai kai kamfanin Facebook cikin jerin manyan kamfanonin da ake ji da su a duniya.
Cikin wannan makon ne ake kyautata tsammanin Facebook zai sanar da wasu nasarori da ya samu, wanda suka hada da ‘karin samun kudin shiga. Ana kuma tsammanin rahotan da ke nuna cewa yawan mutanen da ke shiga shafin Facebook a duk wata sun kai Biliyan 1.9 cikin watanni ukun da suka gabata, cikin ‘yan makonni masu zuwa ne kuma ake sa ran mambobin kamfanin za su cika Biliyan biyu.
Sabanin yadda aka zata Facebook ya tsallake wasu kaluble masu yawa, ya kuma ci gaba da samun sabbin masu amfani da shafinsa, cikin watannin da suka gabata kamfani ya samu ‘karin mutane masu yawan gaske.
Amma duk da haka, masu fashin baki sunyi imanin cewa tabbas dole ne kamfanin ya fara samun koma baya nan gaba.
An yi hasashen cewa a rahotan da Facebook zai fitar na kudaden shiga da yake samu, zai sami ribar Dala Biliyan 3.3.
Duk kuwa da matsin lamba da kamfanin ke samu bai hana shi ci gaba da bunkasa ba, a baya-bayan nan ne ake ta cece-kuce kan ganin cewa Facebook na duba duk wasu abubuwa da mutane ke sakawa a dandalinsa.
Shugaban Facebook Mark Zuckerberg, ya yi alkawarin tashi tsaye wajen shawo kan matsalar aikata ta’addanci ta kan Facebook live, da kuma yada labaran ‘karya.
Your browser doesn’t support HTML5