Facebook: Kotun Tarayyar Turai Ta Yanke Hukuncin Kare Kanta Daga Batanci

Wani taron kungiyar Tarayyar Turai

Babbar Kotun Tarayyar Turai ta yanke hukuncin cewa za a iya tilasta wa kamfanin abota na Facebook da ya cire duk wani abu da aka wallafa a duk duniya ba bisa ka’ida ba, indan har ya sabawa dokar wata kasa da ta kasance mamba a kungiyar Tarayyar Turai.

Shi dai wannan hukunci da Babbar Kotun Tarayyar Turai ta yanke, babu damar da za a iya daukaka shi.

Hukuncin ya samo asali ne daga wata kara da tsohuwar shugabar Jam’iyyar Green Party a kasar Austriya, Eva Glawischnig-Piesczek ta shigar, wacce ta nemi kamfanin na Facebook ya sauke kalaman batanci da aka buga game da ita.

Wata kotu a kasar ta Austriya, ta ce kalaman sun take dokar da ta haramta bata sunan wani.

Yawancin kafofin sada zaumunta kamar Facebook, galibi sukan cire duk wani abun batanci da ya saba dokar wata kasa.

Hukuncin na jiya Alhamis zai tilasta musu yin hakan a duk fadin duniya.