Facebook, Instagram Da WhatsApp Sun Katse

Facebook

A wani sakon Twitter da ya aike, Facebook wanda shi ya mallaki shafukan sada zumantar baki daya ya nemi afuwar masu amfani da su inda ya kara da cewa yana kokarin shawo kan matsalar.

Rahotanni daga sassan na duniya na cewa manyan shafukan sada zumunta na Facebook, WhatsApp da Instagram ba sa aikin yayin da miliyoyin mutane a sassan duniya ke kokari su yi amfani da su.

A yankin Amurka lamarin ya faru ne da safiyar ranar Litinin da misalin karfe 11:45 inda manyan shafukan suka daina aiki kwata-kwata.

A Najeriya, wakiliyar Muryar Amurka Baraka Bashir da ke Kano a arewacin kasar, ta tabbatar da cewa shafukan sun daina aiki a lokacin da muka tuntube ta.

Kazalika wakilanmu da ke Abuja sun ce wadannan dandali na sada zumunta duka ba sa aiki.

A shafinsa na Twitter, kamfanin na Facebook ya ce ya samu labarin wannan lamari, kuma yana iya bakin kokarinsa “wajen ganin ya shawo kansa ba tare da bata lokaci ba, muna neman gafara kan wannan lamari.”

Akalla mutum biliyan 2.85 ke amfani da shafin Facebook a duk wata a cewar kamfanin kididdiga na Statista.

Shi kuwa WhatsApp an yi kiyasin yana da mutum biliyan 2 da suke amfani da shi a duk wata yayin da Instagram ke da mutum sama da biliyan daya.

Kamfanin bai fadi dalilin da ya haifar da wannan katsewa ba, duk da cewa ya ce yana kokarin shawo kan matsalar.