Ethiopia: Kamfanin Jiragen Sama a Karon Farko Ya Bar Mata Tuka Jirgi Zuwa Thailand

Daya daga irin jiragen da kamfanin ke dasu kamar wannan Boeng 787 Dreamliner

A karon farko a tarihin kamfanin jiragen sama na Ethiopia mata zalla suka yi aiki. A daren jiya Laraba ne jirgin ya tashi daga Habasha zuwa Bangkok, na kasar Thailand.

Kamfanin jiragen saman yace ya dauki wannan matakinne domin karfafawa mata gwuiwa, da kuma kwadaitawa 'yan matan Afirka shiga aikin jiragen sama.

Shugaban kamfanin jiragen saman Ethiopia Tewolde Gebremariam, yace jawo hankalin mata su shiga wannan fanni yana daga cikin dalilanda kamfanin ya dauki wannan mataki.

Ta ko wani bangare na aikin jirgi, a wannan tashin, mata ne zalla suke aikin, kama daga tsara tafiyar, gyare-gyare, da matuka, hatta da masu bada izinin tashi ko sauka duka mata ne.

Lokacinda jirgin zai sauka a Bangkok ma, ma'aikatan shige da fice dana kwastam duk mata ne.

Kamfanin jiragen sama na fasinjan Ethiopia, yace kashi daya cikin uku na ma'aikatansa duka mata ne. Amma wannan adadi yayi kasa, idan aka koma ta fannin makanikai da kuma matuka.