Ethiopia: An Yi Hasarar Rayuka Sanadiyar Zanga-zangar Kabilar Oromo

'Yan kabilar Oromo dake zanga zanga

'Yan kabilar Oromo na kin amincewa da shirin gwamnati na mayar da gonakansu wuraren gina masana'antu da zummar habaka tattalin arzikin yankin da kuma kasar

Ahalinda ake ciki kuma, hukumomi a Ethiopia watau Habasha, sun ce an kashe mutane a wata zanga zangar nuna rashin amincewa da shirin gwamnati na maida wasu gonaki kusa da babban birnin kasar a zaman wani yanki na kasuwanci.

Ministan yada labarai Getachew Reda, ya fada jiya Litinin cewa, sai ta yiwu adadin wadanda suka halaka ya haura. Magoya bayan 'yan hamayya suka ce an kashe fiye da mutum 30 a tsawon mako uku da aka kwashe ana zanga zanga, a yankin da ake kira Oromia dake kusa da Addis Ababa, babban birnin kasar.

Masu zanga zangar 'yan kabilar Oromo ne, wadanda suka ce shirin gwamnatin kasar idan aka aiwatar, zai kai ga rasa 'yancinsu da danniya 'yan kabilar wadanda suke da zama a bayan garin Addis Ababa.

Amma gwamnatin kasar ta kare matakin da take shirin dauka da cewa, juya gonakin a gina masana'antu zai kawowa yankin 'yan kasuwa wanda hakan zai sa mutanen su amfana.

'Yan hamayya suka ce masu zanga zangar galibi dalibai ne da manoma, ita kuma gwamnati ta ce mutanen "yan gani kashenin-kabilar Oromo" ne, da kuma wasu 'yan banga dauke da makamai.

Kabilar Oromo dake zanga zangar kin amincewa da manufar gwamnati

'YAan kabilar Oromo dake kin amincewa da shirin gwamnatin kasar Ethiopia