Eritrea Ta Zargi Kasar Habasha da Kai Mata Hari

Giram Asmerom, Jakadan Eritrea a Majalisar Dinkin Duniya

Ma'aikatar Yada Labaran Kasar Eritiriya ta fitar da wata takardar bayani, inda ta ke zargin gwamnatin Habasha da kaddamar da harin soji kan kasar.

Kasar Habashar dai ta karyata zargin na takalar fada, ta na mai zargin Eritiriyar da takalo abin da ya haifar da mai da martani daga Habasha.

Takaitaccen jawabin na Ma'aikatar Yada Labaran Eritiriya na cewa harin ya auku ne a yankin Tsorona. Tsorona dai wani kauye ne da ke daura da kan iyaka, mai tazarar kilomita 35 daga Adigrat, wani garin da ke cikin kasar Habasha a yankin Tigray.

Ministan Sadarwar Habasha Getachew Reda ya ce sojojin Eritiriya, wadanda su ka fito daga yankin Tsorona, sun yi wasu take-take na takala, wadanda su ka janyo martani daga bangaren Habasha. Bai yadda cewa wani babban fada suka yi ba.

"Wata 'yar tayar da gira ce kawai, saboda bangaren Eritiriya ya dau wani mataki mai cike da shakku saboda halin da ake ciki, ganin cewa rabon sojojin Eritiriya su ma fita daga ramukan buyansu an jima," a cewar Reda, wanda ya yi magana da Muryar Amurka daga Jamus.