Dan wasan Ivory Coast Eric Bailly, yana shirye shiryen barin kungiyar kwallon kafa ta Manchester United a watan Janairu 2019, da zarar an bude hada hadar 'yan wasan kwallon kafa na duniya inda kulob din Arsenal da Tottenham suke tunanin cewa suna sha'awar dan wasan mai shekaru 24 da haihuwa.
Manchester City, Tottenham, Barcelona da kuma Juventus suna son dan wasan Paris St-Germain na tsakiya na Faransa mai suna Adrien Rabiot, mai shekaru 23 da haihuwa.
Dan wasan Galaxy LA Zlatan Ibrahimovic, ya zura kwallonsa ta 500 a tarihin wasannin sa da ya fafata a duniya a wasan da suka yi da kungiyar Toronto inda suka doke su daci 5-3.
Kocin Manchester United, Jose Mourinho, yana shirye shiryen dauko dan wasan Arsenal a watan Janairu, dan wasan Jamus mai shekaru 29, Mesut Ozil.
Kungiyar Juventus ta sanya dan wasanta dan kasr Argentina mai shekaru 24 da haihuwa Paulo Dybala. Manchester United ta nemi dan wasan tsakiya na Faransa Paul Pogba, mai shekaru 25, zuwa Turin a cikin yarjejeniyar da ta kai kimanin fan miliyan £ 150m a Janairu.
A halin yanzu kuma, Pogba yana son kara yarjejeniyar a Old Trafford - amma sai in Mourinho ya bar wajan kuma a maye gurbinsa da tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane.
Chelsea, za ta bude tattaunawa kan yarjejeniyar shekaru biyu tare da dan wasan tsakiya mai shekaru 31 da haihuwa, David Luiz, wanda kwangilarsa zata kare a karshen kakar wasa ta bana.
Your browser doesn’t support HTML5