Equatorial Guinea Ta Lallasa Super Falcons

Super Falcons

An fitar da ‘yan wasan kwallon kafar mata super Falcons daga shiga gasar wasanin Olympics da za’a yi a shekarar 2016, a yayin da Equatorial Guinea ta lallasa su da ci 2 – 1 cikin Karin lokaci na wasan da aka buga ranar lahadin da ta gabata.

Wannan wani abin takaici ne ga manyan ‘yan wasan kungiyar kwallon kafar mata ta Najeriya, bayan sun fara taka rawar gani da farkon wasan, daga karshe kuma, suka fadi warwas a filin wasan Estadio de Bata.

Ngozi Okbi wadda ta rattaba hannu da kulob din Washington Spirit ce ta fara ba kungiyar ‘yan wasan Super Falcons damar fara jan ragamar wasan cikin minti na goma sha takwas da farko.

‘Yan wasan da suka marabci kungiyar ta super Falcons, ba su sami yin kunnen doki da ‘yan wasan na super Falcons ba sai a cikin minti na 86 na karshen wasan, wanda hakan ya sa wasan ya karke da Karin lokaci

A cikin lokacin da aka kara na wasanne Nzalang Nacional ta dauki ragamar nasarar lashe wasan acikin minti na 112.

Wannan shine karo na biyu da zakarun ‘yan wasan na Afirka ke faduwa ba nauyi, kamar yadda suka rasa bugun daga kai sai gola a wasan su da Kamaru, a wasan shiga jerin wasannin London na shekarar 2012.

A yanzu haka Equatoria Guinea zata fafata da Afirka ta kudu a wasan zagayen karshe na samun tikitin shiga wasan Olympics.