‘Yan wasan kungiyar kwallon kafar Enugu Rangers sun tashi zuwa kasar Misira inda zasu fafata da kungiyar kwallon kafar Zamalek na kasar ta Misira.
Amma ‘yan wasan basu amince su yi tafiyar ba sai da aka ba kowane dalar Amurka $730, kudin alawus din tafiyar su, ana sa ran cewa ‘yan wasan zasu sauka kasar Misira a yau juma’a gabanin wasan da zasu buga ranar lahadi a ci gaba da gasar zakaru ta CAF.
Wata majiya ta fadawa mujallar Complete sports ta Najeriya, cewa ‘yan wasan sun ce suna fatan hukumar kungiyar zata cika alkawarinta na basu ragowar kudaden da suke bin kungiyar.
Zasu buga wasan ne a filin wasa na El-Arab, dake Alexandra ta kasar ta Egypt ne kuma alkalin wasa Daniel Bennett, dan kasar Afirka ta kudu shi zai yi alkalancin wasan. Enugu Ranger zasu karbi bakunci Zamalek a mako mai zuwa a Najeriya.
Your browser doesn’t support HTML5