Embalo Ya Sha Alwashin Magance Matsalolin Guinea Bissau

Umaro Sissoko Embalo,

Sabon shugaban kasar Guinea Bissau, kuma tsohon Firai Minista, Umaro Sissoko Embalo, na murnar lashe zaben da aka yi a kasar, yayin da bangaren adawa ke ikrarin cewa an tafka kurakurai a zaben.

A jiya Laraba hukumar zaben kasar ta ayyana Embalo a matsayin wanda ya lashe zaben da kaso mafi tsoka, wanda hakan ya dara makin abokin hamayyarsa, Domingos Simoes Pereira na jam’iyyar PAIGC.

Sabon shugaba Embalo ya ce kasar Guinea Bissau, "za ta sauya akalar tafiyarta, domin lokaci ya wuce da kowa zai rika yin abin da ya ga dama."

Sai dai duk da cewa abokin hamayyarsa Pereira na zargin an tafka madugi a zaben, babu wani daga cikin tawagogin da suka sa ido kan zaben, da ya ba da rahoton cewa akwai kurakurai a zaben,.

Sannan wakilin Majalisar Dinkin Duniya a zaben na Guinea Bissau bai soki sakamakon zaben ba.