ZABEN2015: El-Rufa'i Na Kan Gaba Da Kuri'un Kaduna

Nasir El-Rufai

Ya zuwa yanzu alkalumman kuri’un da aka kada a jihar Kaduna na zaben gwamna sun nuna cewa tsohon ministan birnin tarayyar Najeriya Malam Nasir Elrufa’i na jam’iyyar adawa ta APC yana kan gaba a bisa abokin takararsa Mukhtar Ramalan Yero wanda shine gwamnan jihar.

Hukumar zaben jihar kaduna ta bayyana sakamakon wasu kanan hukumomin guda goma sha biyar da suka hada da Soba, Kudan, Makarfi, Kajuru, Kubau, Kauru, Kagarko, Ikara, Sabon Gari, Kaduna ta Arewa, Jama’a, Giwa, Igabi, Kaduna ta Kudu da kuma Chikun.

Musa ZUbairu Usman mai fashin bakin siyasa yace abin ba abin mamaki ba ne don kuwa gwamnatin tarayya ita ta haifar da ta Kaduna wanda kosawa da aka yi da waccan gwamnatin ta tarayya ne yasa suka kosa data Kaduna.

Game da maganar rade-radin El-rufa’i na kokarin lashe kuri’un karamar hukumar Zaria sai mai fashin bakin yace, ai ‘yan Zaria na kuka da yadda bas u ga katabus a kasa ba musamman game da maganar ruwan sha a zaria da kewaye.

Idan ba a manta ba dai lakabin da ake wa Malam Nasir din shine ‘Mai Rusau’ wanda ke nuna yadda ya yi rushe rushe a Abuja to mutane su yi hattara, amma masu lura da al’amuran yau da kullum suna ganin maimakon wannan suna yayi masa illa sai ya kara masa farin jin ya kuma zama lakabinsa a bakin jama’a da cewa ‘Kaduna Sai Mai Rusau’.

Abin jira dai a gani shine jiran sakamakon sauran kananan hukumomin na jihar Kaduna da suka rage don jin wanda zai lashe wannan zabe na zama gwamnan jihar Kaduna a Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

ZABEN2015: El-Rufai Na Kan Gaba Da Kuri'un Kaduna - 2'50"