Inda ta kara da yin kira ga sauran kasashen da suke membobin kungiyar da su kara zage damtse wajen ganin an murkushe ta’addanci. Shugaba Sirleaf ta maye gurbin Shugaba Macky Sall na Senegal da ya jagoranci kungiyar.
An gabatar da zabenta ne a babban taron shekara-shekara na ECOWAS da aka yi a cikin karshen makon da ya gabata a birnin Dakar din ta Senegal. Wata sanarwar da ta fito daga ofishin Shugabar, ta bayyana kiran karkare magana.
Game da maganar daukar mataki a dokance don rayawa da kuma kawo gamayyar kasuwanci tsakanin kasashen Afirka ta Yamma. Sirleaf ta kuma yi alkawarin inganta daidaiton hada-hadar kudi.
Inda wani daraktan cibiyar bincike ta kasashen Afrika ta Yamma Ousman Sene ya bayyana cewa, daidaiton hada-hadar kudi ta kasashen, musamman wajen yi kudin da zasu yi amfani bai daya, to zai inganta wannan kuduri na tattalin arzikin nahiya.