EFCC Tana Binciken Wasu Jami'an Hukumar Zaben Najeriya, INEC

EFCC

Tun makon da ya gabata kafofin labarun Najeriya ke yayata jita jitan cewa wai hukumar EFCC tana binciken wasu jami'an hukumar zaben kasar, wato INEC masu dimbin yawa

Muryar Amurka ta tuntubi hukumar INEC domin ta tabbatar da sahiyar gaskiyar maganar cewa ana binciken wasu jami'anta dari da laifukan da suke da alaka da cin hanci da rashawa lokacin zabukan da suka gabata.

Nick Dazan da yayi magana da yawun INEC ya tabbatar da binciken da yace yanzu yana wakana. Yace adadinsu ya fi dari bisa ga kudaden da aka ce an bayar a matsayin cin hanci a zaben 2015.

Yawancin wadanda suke da hannu a lamarin a jihohi suke. Na hedkwatar INEC din wai basu da yawa, kalilan ne. Wasu cikin wadanda ake binciken sun riga sun yi murabus.

Hukumar EFCC ce ta fara gudanar da binciken amma bisa ga bayanan da shugabannin INEC suka samu sun tuntubi EFCC inda suka kara samun karin bayanai akan lamarin. INEC na ba EFCC goyon baya kuma shugaban INEC yace duk wani jami'inta da yayi abun da ba daidai ba zata ladabtar dashi.

Da zara hukumar EFCC ta gurfanar da jami'an gaban kotu to INEC na iya dakatar dasu daga bakin aiki har sai kotu ta gama dasu ko su kansu sun wanke kansu.

Ga rahoton Adamu El-Hikaya da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

EFCC Tana Binciken Wasu Jami'an Hukumar Zaben Najeriya, INEC - 4' 07"