Wata babbar kotun tarayya a Ibadan ta yanke wa tsohon shugaban Cibiyar Binciken Aikin Gona dake Ibadan, Farfasa Ogunbobade hukuncin daurin shekaru arba’in a gidan kaso, yayinda shi kuma akawunsa, aka yanke mishi hukuncin daurin shekaru 40.
Haka kuma kotun ta daure wani na ukunsu shekaru hudu kawai.
Hukumar EFCC ce ta shigar da karar inda ta zargesu da wawure Naira miliyan dari da saba’in da bakwai da kuma hada baki da batar da sawun wasu kudaden na daban.
Mai shari’a Ayo Emmanuel yace mai gabatar da kara ya gamsar da kotun cewa wadanda ake zargin sun aikata laifukan kasa zuba Naira miliyan dari shida cikin asusun kasa.
Lauyan daya daga cikin wadanda ake zargin, Tunde Olupona, yace hukuncin zai zama darasi ga wasu masu son karkata kudaden jama’a a nan gaba.
Ga rahoton Hassan Umar Tambuwal da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5