Duk da hukumar EFCC ta musanta cewa alkalin alkalan Najeriya Walter Onnoghen da wasu manyan mutane na cikin mutane sama da dari da take bincike amma ta ce wasu daga cikin binciken na matakin farko ne.
Kakakin hukumar Mr. Wilson Uwujeren ya musanta labarin wata sanarwa.
A zantawar da mukaddashin hukumar EFCC Ibrahim Magu ya yi da Muryar Amurka yace akwai muhimman tuhume tuhume da suka yi amma saboda lamarin shari'a ba zasu bayyana sunaye ba.
Yana mai cewa sun samu kudi kimanin Nera biliyan dari hudu da tara. Sun samu dala miliyan sittin da tara da rabi.Sun samu kudaden ne daga mutane da yawa. Tun da kuma yawancin lokaci suna kotu ba zasu iya bayyana sunayen mutane ba, inji Ibrahim Magu.
Kawo yanzu sun samu hukuncin kararraki 137 a wannan shekarar kawai. Sun samu cigaba irin wanda ba'a taba samu ba a tarihin yaki da cin hanci a kasar.
Ga rahoton Saleh Shehu Ashaka da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5