EFCC Ta Damke Wani Matashi A Bisa Zambar Naira Milyan (7,000,000)

Hukumar EFCC, ta damke wani matashi mai shekaru ashirin da shida, dalibin jami’ar Ado-Ekiti, a bisa zargin zamba, ta hanyar yanar Gizo, na kudi fiye da Naira milyan bakwai.

Matashi mai suna Obohor John Damilola, ya zambaci mutane hudu, a shafin zawartaka na sojoji, inda ya nuna kansa a matsayi sajan Sojan Najeriya, mai suna Frank Mcghee.

Ofishin EFCC, dake kula da yankin Ibadan, wanda jami’anta ne su suka damke matashi, tace ta bi sahun matashi ne biyo bayan wani gudane gudane a wani Banki, a Ado-Ekiti, ta inda yay a karbi kudi fiye da Naira miliyan bakwai.

Wadanda ya zambata sune L.D Marte, miliyan shida da dubu dari biyu da goma sha shida da dari bakwai da talatin da biyu, sai P. Martinez, dubu dari shida da saba’in da biyu da Dario takwas da tamanin da bakwai da kuma E. Rosales, dubu talatin da sittin da biyar sai R.Rosario Naira dubu dari biyar da talatin da hudu da daridaya da goma sha biyar.

Obohor da ake zargin ya amsa laifinsa yana cewa ya fara zambatar muta ne domin ya sami kudi ya biya kudin makarantarsa.