EFCC, ICPC, Kungiyar Gwamnoni Zasu Gana Da Shugaban Ma'aikatan Gwamnati

EFCC

Kungiyar gwamnonin Najeriya zata gana da EFCC da ICPC domin nazari cikin tsanaki kan yadda gwamnoni su ke kashe kududaden da gwamnatin tarayya ke ware musu na shawo san satsalolin tsaro

Ana sa ran cewa, gwamnonin Najeriya 36 zasu gana da EFCC da hukumar ICPC da shugaban ma’aikatan fadar gwamnati gobe Talata inda ake sa ran zasu tattauna a game da kudin da ake ware wa jihohi domin magance matsalolin tsaro wato security votes wanda ake samun shakku a game da yadda gwamnonin su ke kasea wadannan kudade.

Baya da wadannan hukumomi masu sa ido akan masu yi wa kasa ta’anniti EFCC, da kuma hukuma mai sa ido akan cin hanci da rashawa, ICPC, da kuma wasu hukumomin gwamnati hudu da suka hada da kungiyar gwamnonin Najeriya NGF, babban bankin Najeriya CBN, hukumar tattara haraji ta kasa FIRS, da kuma hukumar dake bin diddigin hada-hadar kudade NFIU, zasu kasance a wurin taron.

Shugaban ma’aikatan ya bayyana batun duba yiwuwar fadada dokar yin hada-hadar yau da kullum da tsabar kudi wanda ya fara aiki daga lokacin da gwamnatin Najeriya ta sauya fasalin kudadenta a shekarar da ta gabata domin tabbatar da cewa, duk ‘yan kasar sun shiga tsarin hadar-hadar na zamani nan gaba. Ya kuma bayyana cewa, wata wasikar da ke dauke da sa hannun shugaban NFIU Moddibo Hamma Tukur wanda ya aikawa shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya mai dauke da kwanan wata 30 ga watan Maris na bana ne ya sanar da kuma gayyatar mahalarta.

A bisa gayyatar taron da shugaban babban darektan kungiyar ma’aikatan ya aike, za a gudanar da taron ta yanar gizo.

Za kuma a duba yiwuwar daidaita tsarin tattara haraji da kuma yin garambawul a tsarin.