EFCC da Kungiyar Gwamnonin Najeriya Sun Shiga Wata Takunsaka

EFCC

Shugaban EFCC na riko Ibrahim Magu da kungiyar gwamnonin Najeriya sun shiga takunsaka saboda wani zunzurutun kudi na N388b da aka mayarwa Najeriya daga bashin da ta biya wanda kuma ta rabawa jihohi

Shugaban EFCC na riko Ibrahim Magu yana gudanar da bincike akan yadda gwamnoni suka yi anfani da kudin.

Wannan lamarin da Ibrahim Magu yake bincike ya zo daidai lokacin da kujerarsa take tanga-tanga domin majalisar dattawan kasa dake da alhakin tabbatar masa da kujerar ta mayar da sunasa ga shugaban kasa bisa ga zargin da hukumar tsaro ta DSS tayi na cewa yana da hannu a cin hanci da rashawa.

Baicin hakan ana rade-radin cewa gwamnonin na iya yi masa zagon kasa su hana majalisar dattawa tabbatar dashi.

A firar da aka yi da gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari wanda shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya ya musanta rade-radin cewa sun shiga takunsaka kuma suna goyon bayan majalisa na kin amincewa da nadinsa.

Gwamna Yari yace basu yanke shawara akai ba tukunna saboda ita EFCC tace tana kan bincike. Yace zasu dakata har sai sun fitar da sakamakon binciken kafin gwamnonin su mayar da martani.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

EFCC da Kungiyar Gwamnonin Najeriya Sun Shiga Wata Takunsaka - 2' 03"