Abun takaici ma shi ne yadda wadanda ake tuhuma suke samun beli cikin dan karamin lokaci lamarin da kan sa akan manta wadanda aka gurfanar gaban kotu.
Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya wato EFCC tace ba zata sanya baki akan yadda kotuna ke gudanar da ayyukansu ba ko kuma yadda suke ganin jinkirin da ake samu a shari'un.
Mai magana da yawun hukumar EFCC yace ba zai yi magana akan batun ba amma sun san kararrakin da suka gabatar na ciga.
Akan bukatar da su EFCC suka gabatar na samun kotu na musamman da zai saurari kararrakin cin hanci da rashawa, sai mai magana da yawun hukumar yace wannan lamari ne na 'yan majalisun tarayyar kasa su aiwatar idan sun ga dama.
Tsawon lokacin da kotuna ke dauka kan kararraki da suka jibanci cin hanci da rashawa ba tare da cimma wani hukumci ba ya sa wata kungiya Corrupt Free Society ta nemi goyon bayan kowane bangaren Najeriya domin a hukumta duk wanda aka samu da wawure dukiyar al'umma.
Injiniya Ahmed Zakari Guroje shugaban kungiyar yace yana son 'yan Najeriya su fahimci cewa fada da cin hanci da rashawa ba na Muhammad Buhari ba ne shi kadai, fada ne duk wani dan Najeriya dake da kishin kasa. Yace ya zama wajibi duk 'yan kasar su tashi su yaki cin hanci da rashawa.
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5