Eden Hazard: Babu Kanshin Gaskiya Ko Zan Koma Wata Kungiya

Dan wasan Chelsea Eden Hazard ya karyata rade radin da akeyi na cewar ya kammala dukkan yarjejeniya tsakaninsa da kungiyar Real Madrid kan batun komawarsa kulob din a karshen kakar wasa ta bana.

Inda wasu kafafen yada labarai dake kasar Spain suka ruwaito, cewa dan wasan ya amince da yarjejeniyar komawa Real Madrid har na tsawon shekaru biyar.

Bayan haka kuma cikin yarjejeniyar kungiyar ta Real Madrid ta amince za ta fifita albashinsa fiye da dukkanin wani dan wasa a kungiyar.

An dai dade ana alakanta dan wasan na Chelsea da zuwa kungiyar Real Madrid a baya, amman har ya zuwa wannan lokaci ba'a samu tabbaciba.