Ecuador Da Najeriya Na Shirin Fara Huldar Kasuwanci

Rafael Correa shugaban kasar Ecuador

Kasar Ecuador da Najeriya na shirin kulla huldar kasuwanci da Najeriya a fannin kasuwanci da saka hannayen jari a cewar Jakadan kasar.

Jakadan ya bayyana hakan ne yayin wata ziyara da ya kai wa gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje.

Jakadan ya ce a kokarin da kasarsa ke yi na kulla danganta da kasashen nahiyar Afirka ta fannoni daban daban ya sa a shekarar 2015 kasar ta bude ofisoshin jakadanci a wasu kasashe hudu da suka hada da Najeriya.

Kafa ofisoshin zai ba kasar damar karfafa tare da farfado da alakarsu da nahiyar Afirka, inji jakadan.

Ya kuma yi tsokaci akan yadda kafofin labarai za su taimaka wurin cimma muradun da suka sa a gaba.

Jakadan ya samu ganawa da gwamnan Kano Dr Abdullahi Ganduje inda suka tattauna game da kasuwanci da saka jari da kuma fasahar samar da lantarki.

Daga bisani jakadan ya ziyarci Mai Martaba Sarkin Kano Malam Muhammad Sanusi II kafin ya koma Abuja.

Ga karin bayani a rahoton Mahmud Ibrahim Kwari:

Your browser doesn’t support HTML5

Ecuador Da Najeriya Na Shirin Fara Huldar Kasuwanci - 2' 13"