Kungiyar bunkasa tattalin arzikin afrika ta yamma (ECOWAS) ta tsananta kokarin da take yi a zahiri wajen kaddamar da kudin bai daya, Eco, ga yankin sakamakon daidaiton da aka cimma akan aiwatar da umarnin da aka bayar yayin karo na 65 na babban taronta.
An bayyana hakan ne a cikin sanarwar bayan taron da aka fitar a karshen karo na 65 na taron shugabannin kasashen ecowas daya gudana a birnin Abuja a Lahadin da ta gabata.
A baya kungiyar ECOWAS mai mambobi 15 ta yi shirin kaddamar da kudinta a shekarar 2020, sai dai barkewar annobar Korona ya haifar da tsaiko.
Sabuwar ranar da aka tsayar da kaddamar da takardar kudin ta koma 2027.
Kungiyar ta bayyana cewar ta amince da tsarin da kwamitin zaben kasashen da zasu jagoraanci kaddamar da kudin Eco din ya gabatar da kuma wadanda zasu shigo cikin shirin anan gaba.