Kungiyar habaka tattalin arzikin Afrika ta yamma ECOWAS a takaice, ta sabunta alkawarin tura sojoji Mali, domin taimakon gwamnatin kasar sake kwato yankunan arewaci kasar daga kungiyoyin 'yan tawayen Musulmi.
Shugaban kwamitin ECOWAS, Kadre Desire Ouedraogo yace a shirya kungiyar ECOWAS take, ta tura sojojin shiri kota kwana a Mali, da zarar gwamnatin rikon kwaryar kasar ta bukaci haka
Wannan alkawari yana kunshe ne ciki sanarwar yin marabar da komawar shugaban rikon kwarya Dioncounda Traore, wanda yaje kasar Faransa neman jinya bayan da masu zanga zangar kin jinin gwamnati suka nankada masa kashi.
A ranar Lahadi shugaba Traore ya bada sanawar shiri yiwa gwamnatin rikon kwarya garambawul kuma ya bukaci taimako daga waje na sake kwato arewacin kasar.
Drektan harkokin siyasar kungiyar ECOWAS Abdel Fatau Musah yace ana shirye shirye tura tawagar wakilan hadin gwiwa ta kungiyar ECOWAS da Majalisar Dinki Duniya da kuma kungiyar kasashen Afrika domin nazarin irin ci gaban da aka samu wajen kafa sabuwar gwamnati.
Ya fadawa sashen turanci na Muryar Amirka cewa, tsohon shugaban mulkin sojan Mali, yana kokarin yin shishigi a harkokin kasar bayan ya mika mulki hannun gwamnatin rikon kwarya, bayan juyin mulkin da aka yi a kasar a watan Maris.