Ebola: Uganda Ta Mayar Da Wasu 'Yan Kasar Congo Gida

Wata cibiyar binciken alamomin cutar Ebola mai saurin kisa

Hukumar ta kuma ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da wadanda ake tunanin suna dauke da ita, ya haura mutum 3,000.

Kasar Uganda ta mayar da wasu mutane biyar ‘yan asalin Congo zuwa kasarsu.

Ana fargabar mutanen sun yi cudanya da wata yarinya mai shekaru tara da ta rasu sanadiyyar cutar Ebola a Gundumar da ake kira Kasase da ke yammcin kasar ta Uganda.

A ranar Laraba, yarinyar wacce ita ma ‘yar asalin kasar Congo ce, ta yi tafiya da mahaifiyarta daga yankin Goma, suka shiga kasar ta Uganda ta kan iyakar Mponwe domin neman magani.

Daga karshe an kebe ta, aka kuma mayar da ita wani asibiti da ke kusa da yankin domin a yi mata magani, inda wani gwajin da aka yi mata ya nuna lallai cewa tana dauke da kwayar cutar ta Ebola.

“Abin takaici, yarinyar ta riga mu gidan gaskiya da safiyar jiya Juma’a, kuma bisa bukatar da mahaifinta ya mika, ana shirin mika gawarta domin a mayar da ita Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo domin a yi mata jana’izar.” In ji Dr. Joyce Moriku Kaducu, karamar ministar lafiya a kasar ta Uganda.

Adadin Wadanda Suka Kamu Da Cutar Ya Haura 3,000

A halin da ake ciki kuma a kasar ta Jamhuriyar Dimkoradiyyar Congo, adadin mutanen da suka mutu sanadiyyar cutar ta Ebola ya kai mutum 2,000, a cewar hukumar lafiya ta duniya WHO.

Hukumar ta kuma ce adadin mutanen da aka tabbatar sun kamu da cutar da wadanda ake tunanin suna dauke da ita, ya haura mutum 3,000.

Ko da yake, cutar ta yadu zuwa wasu sabbin yankunan kasar ta Congo, hukumar ta WHO ta ce, har yanzu adadin mutanen da ke kamuwa da ita cikin mako guda na nan a 77 kamar yadda yake a baya cikin wata daya da rabi da ya gabata.

Ita dai kwayar cutar Ebola, ta ci gaba da yaduwa, duk ko da cewa an rigakafin cutar, wacce ya zuwa yanzu an yi wa mutum dubu 200,000 allurarta a gabashin kasar ta Congo.