Ebola Ta Kashe Mutane 200 a Kasar Kongo

  • Ibrahim Garba

Masu yaki da Ebola a kasar Kongo

Ga dukkan alamu, hankalin 'yan Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo da ma na makwabtan kasashe zai sake tashi saboda sake bullar annobar mugunyar cutar nan ta Ebola. Tuni ma ta hallaka daruruwan mutane a wannan karon.

Bullar annobar Ebola a yakin gabashin Janhuriyar Dimokaradiyyar, ta yi sanadin mutuwar mutane 200. Hukumomi sun ce zuwa yanzu mutane 300 ne su ka mutu tun bayan barkewar annobar a cikin watan Agusta.

Ma'aikatar Lafiyar Jahar ta ce rabin wadanda su ka kamu da cutar a Beni su ke, garin da ke dauke da mutane 800,000 a lardin Kivu na Arewa.

Annobar ta fi bulla ne a yankin da aka fai tashe-tashen hankula, inda kungiyoyin mayaka da dama ke kai komo. Ala tilas cibiyoyin agaji su ka dakatar - ko kuma su ka sassauta - ayyukansu a lokuta da dama tun bayan bullar annobar.