Ebola: Rwanda Ta Rufe Kan Iyakarta Da Congo

Oliver Nduhungirehe, karamin ministan Harkokin Waje na kasar Rwanda, ya fada a yau Alhamis cewa, gwamnatin kasar ta rufe iyakarta da ke wajen garin Gisenyi a arewa maso gabashin kasar.

Kasar Rwanda ta rufe iyakarta da Jamhuriyar Dimokradiyyar Congo yayin da Congon ke kokarin shawo kan matsalar barkewar cutar Ebola a baya-bayan nan.

Wannan na zuwa ne bayan da aka sami rahoton mutum na uku da ya kamu da cutar a birnin Goma da ke bakin iyakar kasar.

Oliver Nduhungirehe, karamin ministan Harkokin Waje na kasar Rwanda, ya fada a yau Alhamis cewa, gwamnatin kasar ta rufe iyakarta da ke wajen garin Gisenyi a arewa maso gabashin kasar, wato garin da ya hada iyaka da garin Goma.

Akalla mutane sama da miliya ne ke zaune a garin Goma, kuma kullum dubbai kan tsallaka zuwa cikin Rwanda daga garin.

Jami’an kiwon lafiya a kasar Congo sun tabbatar da cewa diyar wani mutum da ya mutu sakamakon cutar ta Ebola a farkon makon nan, ta na nuna alamun kamuwa da cutar.

An dai gano cewa mutumin na dauke da cutar ce a ‘yan kwanaki, bayan isarsa garin Goma daga wani kauye a wani Lardi da ake kira Ituri a arewa maso gabashin kasar.