Duniyar Fina Finai Tare Da Tahir M. Tahir

Jarumin Wasan Fina Finai Tahir M. Tahir

A wannan satin shirin Duniyar Fina Finai na Dandalin VOA ya samu bakuncin shahararren Jarumi kuma Uba a harkar shirya fina finai, Tahir M. Tahir wanda aka fi sani da “Gwamna Ka’ida” an faro da shi a jiya, kuma ake damawa shi a yau, kana kuma yake fatan a dama da shi a gobe.

Idan za’a iya tuna fim din “Gaskiya Dokin Karfe” da aka fitar kusan shekaru goma sha daya, a nan ne Tahir M. Tahir ya fito a Gwamna Ka’ida, tun daga nan sunan ya bishi. Tahir yace yanda yaga Malamin sa Kasimu Yaro tare da Mallam Mamman suna wasan kwaikwayo shine ya bashi sha’awa ya kuma jawo hankalinsa ga wannan sana’a.

Tahir dai ya fara harkar wasan kwaikwayo a shekara ta 1972 da wata kungiya mai suna Gyaranya, wadda daga baya ta koma Jan Zaki. Alokacin dai suna wasan Dabe, wanda daga baya suka fara wasan su a gidan Talabijn da Radiyo.

“An sami cigaban mai hakan rijiya” inji Tahir, alokacin da wakiliyar Dandali Baraka Bashir ta tambayeshi yadda zai kwatanta harkar fim a baya da kuma yanzu? Inda yace ada akwai tarbiya amma yanzu babu.

Domin jin cikakkiyar hirar da Gwamna Ka’ida, danna sauti.