Shirin duniyar fina finai na wannan makon ya sami bakuncin Jaruma Jamila Umar Turaki, wadda aka fi sani da Jamila Nagudu, inda ta bayyana wa wannan filin dalilin dayasa ta fara harkar fim.
Jamila tace wane abu ne ya faru a unguwar su wato a makwabtansu sai kuma ta ga anyi irin sa a cikin wasan fim, kuma wadda take yin irin abin ga abinda ya faru da ita, kuma ga sakamakon ta a cikin fim din, hakan ne yasa ta gano cewa ashe ‘yan fim fadakarwa suke yi. Hakan ne yasa mata sha’awa yin wasan fim domin bayar da ita ma tata gudunmawar wajen fadakarwa da wa’azantarwa.
Yanzu haka ta shafe shekaru tara zuwa goma tana wannan sana’a ta wasan fim, Jamila ta fito a fina finai masu yawa, fim din “Jamila Da Jamilu” na daga cikin fim din da bazata taba mantawa da shi ba a rayuwar ta kuma take afahari da shi.
Kasancewar a baya mutanen da suke harkar fina finai yawancin su suna zaman kansu ne, to kalubalen da suke fuskanta a yanzu shine mutane na yiwa duk masu wannan sana’a ganin cewa suma zaman kansu sukeyi, alhalin su na zaune ne a gidan iyayen su sai aiki yazo za’a kira su domin su fito suyi.