A shirin duniyar fina finai Dandalin VOA ya zanta da Hadiza Aliyu Gabon, jarumar fina finai wadda ta fara wannan sana’a tun shekara ta 2009, ko da yake ta fara da wasan kwaikwayo tun tana karama amma fa na dandali wanda akeyi a zangon karshe na karatu.
Wakiliyar Dandalin VOA Baraka Bashir ta tambaye ta komai ne ne ya ja hankalin ta fara sana’ar fim? Inda tace tun tana karama take da sha’awar hakar fim, saboda son wannan sana’a da ta keyi a duk lokacin da suke ainishin inda ake ‘daukar hotan bidiyon tana jin ta ne tamkar a gidan su take.
Fina finan da ta fito a ciki wadanda suka fito da ita tayi suna kuma suka fi daukar hankalin mutane gudu uku sune Wasila da ‘Yar Maye da kuma Ban Sani Ba. Hadiza ta godewa Allah ga wannan matsayi da ya bata, tana kuma yin fatan alkhairi ga masana’antar fim ta Kannywood.
A bangaren tsegumi kuwa a yau fim din Bori shine na bakwai da yayi nazarin tsanaki kan illar Bori a addinan ce, tare da baiwa matasa illar yin Bori a al’adance da kuma a addinan ce.