Duniyar Amurka: Yadda COVID-19 Ta Ta'azzara Cin Zarafin Mutane a Amurka

Mahmud Lalo

Mahmud Lalo

Annobar Coronavirus da ta karade duniya, ta kara rura wutar wasu matsaloli da dama a zamantakewar al'uma inda a Amurka ta kara jefa wadanda ake cin zarafinsu cikin wani sabon kangin rayuwa kamar yadda bincike ya nuna.

Rahotanni daga wasu manyan biranen Amurka 14, na nuni da cewa, matsalar cin zarafi a tsakanin ma’aurata ko mazauna gida daya ta karu, tun bayan da aka shiga kangin annobar COVID-19, kamar yadda wani sabon bincike ya tabbatar.

A cikin shirin Duniya Amurka na wannan mako, za mu duba yadda cutar ta COVID-19 ta ta’azzara wannan matsala da kuma hanyoyin da ake bi wajen shawo kanta.

Your browser doesn’t support HTML5

Duniyar Amurka: Yadda COVID-19 Ta Ta'azzara Cin Zarafin Mutane a Amurka - 5'50"