Jami’an Amurka sun ce, yawancin masu wannan aiki na kutse, na zaune ne a gabashin nahiyar turai inda suke zaman kansu – yayin da a wasu lokuta ma, akan samu gwamnatocin da ke mara musu baya.
Washington D.C. —
Tun gabanin mamayar da Rasha ta yi wa Ukraine, jami’ai a Amurka suke gargadin cewa akwai yiwuwar a kawowa Amurkar hare-haren yanar gizo ta hanyar yin kutse a na’urorin wasu muhimman wurare a kasar, lamarin da yanzu, ya sa hukumomin tsaron kasar suka tashi tsaye wajen ganin sun yaki masu wannan mummunar dabi’a wadanda kan nemi kudin fansa kafin su bude kutsen da suka yi wa kamfani ko wata ma’aikata. Yau batun da shirin zai yi nazari akai kenan tare da Mahmud Lalo.
Your browser doesn’t support HTML5