DUNIYAR AMURKA: Martanin Amurka Kan Juyin Mulkin Myanmar Da Kama Navalny a Rasha

'Yan sanda cikin shirin dakile boren masu zanga zangar juyin mulki da aka yi a Yangon, Myanmar, Fabrairu. 4, 2021.

Amurka ta bayyana matakana da take shirin dauka kan juyin mulkin da aka yi a kasar Myanmar da kuma shugaban 'yan adawa a Alexie Navalny da hukumomin Rasha suka kama.

Amurka ta ayyana tsare shugabannin fararen hula da sojojin Myanmar suka yi a matsayin juyin mulki, lamarin da ya sa ta ce ta fara yin nazari kan tallafin da take ba kasar wacce ake kira Burma a hukumance.

Hakan na faruwa kuma, yayin da Amurkan ta yi Allah wadai da hukuncin zaman gidan yari na tsawon shekara uku da rabi da wata kotu a Rasha ta yankewa shugaban ‘yan adawar kasar Alexie Navalny.

Yau kan wadannan batutuwan shirin na Duniya Amurka na wannan mako zai mayar da hankali akai tare da Mahmud Lalo.