Wannan lamari ya sa ana tunanin Trump ya karya doka kuma zai iya fuskantar tuhuma a kotu yayin da lauyoyinsa suka nemi wata kotu ta dakatar da nazarin da ake yi kan takardun.
Washington DC. —
Shirin Duniyar Amurka na wannan mako ya mayar da hankali ne kan takaddamar da ta biyo bayan samamen da jami'an hukumar binciken manyan laifuka ta FBI suka gudanar a gidan tsohon shugaban Amurka, Donald Trump, inda ta bankado wasu takardu da ke kunshe da bayanan sirrin tsaron kasa da ake zargin Trump ya debo daga Fadar White House a lokacin da zai bar mulki. Lauyoyin Trump sun ce suna tunanin Trump ya yi hakan ne bisa tsammanin yana da kariya karkashin doka. A yi sauraro lafiya:
Your browser doesn’t support HTML5