Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), jiya Jumma’a, ta kaddamar da wani wurin musanyar bayanai, da fasaha da kuma hanyoyin jinya a yakin da ake yi da ciwon COVID-19, wanda kwayar cutar coronavirus ke haddasawa.
Shugaban hukumar ta WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus da Shugaban Costa Rica Carlos Alvarado, wanda ya kawo wannan shawarar tun asali, sun jagoranci kaddamar da wannan shirin daga birnin Geneva.
Tedros ya ce wannan shirin, wanda ake kira “COVID-19 Technology Access Pool, C-TAP,” wato ma’adanar fasahohin da su ka jibanci yaki da cutar COVID-19, (C-TAP, a takaice), zai kai ga gina ma’adanar kasa da kasa ta fasahohin da su ke da nasaba da riga kafi, da magunguna da kuma hanyoyin jinya a yaki da wannan annobar.
Ya yi kira ga kamfanoni da gwamnatocin da su ka kikiro ingantattun hanyoyin jinya da su bayar da gudunmowar fasahohin kirkiro magungunan ga ma’adanar bayanan, wadda kuma za ta mika ga sauran kamfanonin don su kirkiro karin magungunan.