Shugaba Rouhani Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi yau Lahadi inda yake yabawa janye takunkuman da kasashen duniya suka kakaba musu sakamakon shirinta na Nukiliya.
Amurka da sauran manyan kasashen duniya ne suka dagewa Iran din takunkuman tattalin arziki dana man fetur, bayan da suka karbi rahoton Ma’aikatar Kula Da Harkokin Makamashin Nukiliya ta Duniya akan cewa Farisa ta bada hadin kai game da yarjejeniyar da aka kulla a watan Yulin bara da aka kwashe shekaru biyu ana ja.
Cikin yarjejeniyar har da zuke duk man da ke cikin Nukiliyarta da ma tunbuke duk na’u’rorin hada Nukiliyar, sannan da bada dama ga masu sa ido kan makamashin Nukiliyar duniya don iya shiga cibiyarsu ta Nukiliyar kasar.
Sakataren wajen Amurka John Kerry yace, yanzu ba sauran fargaba ga kawayen Amurka a gabas ta tsakiya.