Mataimakin gwamnan jihar ta Borno Alhaji Usman Mamman Durkuwa ya shaidawa manema labarai sun kammala tsugunar da 'yan karamar hukumar Askira Uba a garuruwansu.
Ya cigaba da cewa nan ba da jimawa ba zasu kammala kwashe mutanen sauran kananan hukumomin zuwa yankunansu. Kazalika gwamnatin jihar zata cigaba da gyare gyaren gidajen mutane da sake gina wasu da ma'aikatu da makarantu da wuraren jin dadin jama'a da 'yan Boko Haram suka lalata.
Alhaji Usman yace suna kyautata zato nan da zuwa watan Disamba zasu mayarda yawancin mutane garuruwansu na asali.
Dangane da jita jita cewa gwamnatin jihar na karban tallafi daga manya manya kasashe da kungiyoyin duniya, Alhaji Usman yace a saninsa abinci da abubuwan da zasu gina jiharsu ake basu. Alhaji Dangote kadai ya basu kudi mai tsoka wanda ya bada nera biliyan biyu amma gwamnan yace baya son kudi a basu kayan aiki. Kawo yanzu Dangote ya basu siminti fiye da tireloli dari hudu.
Duk kungiyoyin dake ikirarin sun kashe kudi sun yi hakan ne wurin sayen kayan magani ko na abinci ko na gine-gine, mataimakin gwamnan kuma yace an gode masu.
Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5