Akan fadin ra'ayi gwamnan Borno Kashim Shetima yace akwai banbanci da kokarin tada fitina kamar yadda matasan Arewa suke neman yi da bayyana ra'ayi.
Gwamnan ya cigaba da cewa duk wanda yake neman tada zaune tsaye bai san tashin hankali ko yaki ba ne. Yana mai cewa duk wanda ya san yaki ba zai yi irin kalamun da matasan arewa suka yi ba na cewa kabilar Igbo su bar jihohin arewa nan da watanni uku.
Acewar gwamna Shettima yau idan akwai wanda ya fi kowa sanin masifar dake tattare da rashin zaman lafiya shi ya fi kowa sani a matsayinsa na kasancewa gwamnan jihar Borno mahaifar 'yan ta'addan Boko Haram. Yace idan yaro yace bai iya gudu ba bai ga abun gudu ba ne. Yace idan matasan arewa basu san ma'anar rashin zaman lafiya ba su nemi wani a jihar Borno yayi masu bayani.
Yace a matsayinsu na kasancewa shugabannin a arewa idan sun ga abun da zai kawo tashin hankali da rashin zaman lafiya dole ne su tsawata saboda banbancinsu ke nan da sauran kasar.
Ga Ibrahim Abdulaziz da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5