Kwamitin kula da sha’anin sojin ruwan Najeriya ya sha alwashin bin diddigin tsare sojan ruwan Najeriya Seaman Abbas Haruna tsawon shekaru shida.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Shugaban kwamitin Yusuf Adamu Gagdi ya ce duk wanda yake da "hannu a al’amarin zai girbi abin da ya shuka."
Wani bidiyon da ya karade shafukan sada zumunta ya nuna nuna matar Abbas Haruna mai suna Hussaina tana zayyana irin halin da mijinta ya shiga bayan da ya samu sabani da shugaban bataliyarsa.
A cewar Hussaina sabanin ya samo asali ne, bayan da mijinta Abbas ya je yin sallah aka zo ba a same shi ba.
Hussaina ta yi ikirarin yadda ta kwashe shekaru shida tana kai komo a tsakanin barikin soji na Abacha a kokarin ganin an saki mijinta wanda ta ce har haukacewa ya yi sanadiyyar garkame shi da aka yi.
Lamarin ya janyo kakkausar suka a sassan Najeriya har ya kai ga hedkwatar tsaron Najeriya ta ce ta kaddamar da bincike a kai.
“Labarin Seaman Abbas Haruna mai cike da abin tausayi wanda aka nuna a shirin ‘Brekete’ ya sa kwamitin majalisar wakilai na sojin ruwan Najeriya ya shiga cikin lamarin da nufin bankado gaskiyar abin da ya faru da kare mutuncin sojojinmu tare da kare hakkin kowane mutum.
“Da kuma bukatar ganin an bankado dukkan jami’an da suke da hannu domin a tabbatar duk wanda yake da hannu wajen take hakkin Seaman Abbas ya fuskanci hukunci.” Gagdi ya ce a cikin sanarwar.