Mukaddashin Darektan hukumar shige da fice da kwastam, Thomas Homan shine ya fada wa ‘yan majilisar wakilai na jamiyyar Democrat su 10 hakan a lokacin da ya gana da su jiya Alhamis a majalisar dokokin kasar.
Sai dai bayan kammala wannan ganawar, dan majilisar wakilai na jamiyyar Democrat daga jihar Texas Joaquin Castro, ya ce burin gwamnatin Trump shine kame bakin haure bakin gwargwadon hali.
Castro ya ce wadanda kawai z asu tsira daga wanna tasku sune yaran da suka shigo Amurka suna kanana kuma yau sun girma kana suna da kariya ta musammam daga wani shirin da tsohon shugaba Barrack Obama ya kirkiro.
A farkon makon da shugaba Donald Trump dai ya hau kan karagar mulki ya ba da umurni na musammam da ya baiwa hukumar shige da fice ikon aiwatar da umurnin.
A halin da ake ciki kuma, daruruwan masu zanga zanga ne suka yi maci cikin dan karen sanyi jiya Alhamis a nan Washington DC, macin da aka kira “ranar da babu baki a Amurka” hadakar da take da goyon baya a duk fadin kasa, har ma wasu masana’antu da ‘yan kasuwa suka rufe kantunansu, domin nuna goyon baya ga bakin.