Duk Kasar Da Babu Kasuwanci Ba Kasa Ba Ce - Indimi

Ziyarar Alhaji Mohammed Indimi zuwa VOA Hausa

Muhammad Indimi yace abinda kawai ya kamata gwamnati ta yi ma dan kasuwa shi ne samar da wuta, da ruwa da hanya
Babban dan kasuwar nan na Najeriya, Muhammad Indimi, yace abin takaici ne, kuma abin kunya, ganin yadda kasa kamar Najeriya ba ta iya samar da wutar lantarki, ko wadataccen ruwa ko hanyoyi ga jama'arta.

Yace rashin wadannan, sune suka sa 'yan kasuwa suka zamo 'yan amshin shatar gwamnati, suka zamo sun dogara kusan kacokam a kan gwamnati domin su samu biyan bukatunsu.

A cikin hirar da yayi da VOA, attajirin yace gwamnati ce ya kamata a ce ta dogara kan 'yan kasuwa, domin duk kasar da babu kasuwanci mai karfi cikinta, to ba kasa ba ce. Yayi misali da kasar Kamaru, inda yace ya tafi har ofishin gwamna a Ngaoundere, amma abin mamaki babu wani dan kasuwa kwaya daya tak dake wurin yana jiran ya nemi kwangila.

Ga cikakken bayanin da Alhaji Indimi yayi cikin wannan hira.

Your browser doesn’t support HTML5

Gwamnati Ya Kamata Ta Dogara Kan 'Yan Kasuwa In Ji Indimi - 2:59