Duk Da Cutar COVID-19 Dole a Ci Gaba Da Harkokin Tattalin Arziki - Rouhani

Shugaban Iran Hassan Rouhani

Dole ne a ci gaba da harkokin tattalin arziki a Iran duk da karuwar yaduwar cutar coronavirus da kasar ke fuskanta, a cewar Shugaba Hassan Rouhani ranar Asabar 11 ga watan Yuli. Ya kuma bada umurnin a hana gudanar da manyan taruka, kamar bukin aure da zaman makoki, don rage yaduwar cutar.

Iran ta sanar da cewa cikin sa’o’i 24 da suka gabata, an samu mutum 2,397 da suka kamu da cutar COVID-19 wasu 188 kuma suka mutu sanadiyyar cutar, yanzu gaba daya mutum fiye da 255,000 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar yayin da mutum 12,600 suka mutu. Kasar, wadda yawan al’umarta ya kai miliyan 80, ita ce ta 9 a adadin mace-mace sakamakon coronavirus a fadin duniya.

Mutum miliyan 12.5 ne aka tabbatar sun kamu da cutar a fadin duniya kuma fiye da mutum 560,000 suka mutu, a cewar kididdigar jami’ar Johns Hopkins.

Annobar COVID-19 a Iran

“Ya zama dole mu hana bukukuwa da taron jama’a da yawa a fadin kasar, inji Rouhani, a cewar wani rahoto na kamfanin dillancin labaran Reuters. Jim kadan bayan ya yi wannan jawabin, ‘yan sandan kasar suka rufe wuraren bukukuwa da zaman makoki har sai yadda hali ya yi.

Shugaban ya kuma ce ta yiwu a soke jarabawar shiga jami’a wannan karon a kokarin da ake yi na dakile yaduwar cutar.