Dubun Wasu Tsagerun Matasa Ta Cika a Adamawa

Jami'an 'yan sanda sun tsaya kuwa da sakateriyar gwamnatin tarayya a Abuja

Cikin kwanakin nan magidanta a jihar ta Adamawa kan kwana ido biyu a bude sakamakon ayyukan mambobin kungiyar matasa da ake kira "yan jagaliyar da ake wa lakabi da 'yan Shila.

Su dai wadannan 'yan Shila da akasarinsu matasa ne, kan tare hanya ko far ma gidaje domin ayyukan tu'annati da suka hada sace-sace da kuma kisa.

Da yake nunawa manema labarai wasu da suka fada tarkon jami'an Civil Defense NSCDC, kwamandan hukumar a jihar, Nuruddeen Abdullahi ya ce sun daura damarar yaki da bata-gari a jihar inda ya kada baki ya ce.

Hukumar tsaron dai ta bukaci jama'a da suke ba da hadin kai, inda Nuruddeen Abdullahi ya yi karin haske.

Yanzu haka dai matsalar a Najeriya na kara ta'azzara, lamarin da ya kai ga kungiyoyi kira na a sauya shugabanin tsaron kasar bisa zargin gazawa.

Sai dai jami'an tsaron sun musanta gazawarsu.

.